Arsenal da Manchester City za su kara ranar Lahadi a wasan karshe a Carabao Cup a Wembley.
Guardiola na fatan zama na farko da zai lashe kofin karo biyar jimilla, yayin da Gunners ke fatan kawo karshen shekara 33 rabon ta da Carabao Cup.
Kuma wanna shi ne karon farko da ƙungiyar da take ta ɗaya a teburin Premier League da wadda take ta biyu da za su kara a wasan karshe a League Cup.
Arsenal ce ta ɗaya a kan teburin Premier League da tazarar maki tara tsakani da Manchester City ta biyu.
Da farko Guardiola ya ci Arsenal wasa tara daga 10, amma kawo yanzu ya fuskanci Arteta karo shida ba tare da nasara ba a dukkan fafatawa.
Wannan shi ne karo na biyu da za su fuskanci juna a bana, bayan da suka tashi 1-1 a Emirates cikin Satumba a Premier League.
Haka kuma Arsenal za ta ziyarci Etihad a wasa na biyu a Premier League a cikin watan Afirilu.