Ko Arsenal za ta koma ta daya a Premier League?

Arsenal za ta karbi bakuncin Aston Villa a Premier League ranar Lahadi karawar mako na 33 da za su fafata a Emirates.

Kungiyoyin biyu sun kara ranar 9 ga watan Disambar 2023, inda Arston Villa ta ci 1-0 ta hannun John McGinn a minti na bakwai da take leda.

Arsenal mai kwantan wasa tana ta biyun teburi da maki 71 da tazarar maki biyu tsakani da Manchester City, wadda ta koma ta daya ranar Asabar, bayan casa Luton Town 5-1 a Etihad.

Arsenal Villa wadda ta buga wasa 32 a Premier League tana ta hudun teburi da maki 60, iri daya da na Tottenham, wadda ta sha kashi a gidan Newcastle United 4-0 ranar Asabar a St James Park.

Bayanai kan raunin ‘yan wasan kungiyoyin biyu:

Jurrien Timber ne kadai ke jinya a Arsenal

Ko da yake Mikel Arteta ya yi korafi kan wasu ‘yan wasa ba sa kan ganiya bayan karawa da Bayern Munich, amma yana fatan kowa zai sa kwazo ranar Lahadi.

Dan kwallon Aston Villa Douglas Luiz, zai fara hutun wasa biyu, sakamakon hukuncin katin gargadi 10 da ya karba a Premier League.

Matty Cash da Clement Lenglet sun koma atisaye, yayin da Tyrone Mings da Jacob Ramsey da Boubacar Kamara da kuma Emi Buendia je jinya.

Bayanai kan karawa tsakanin kungiyoyin biyu:

Arsenal ta lashe wasa biyar daga shida baya a Premier League a gida da ta kara da Aston Villa, wadda ta yi rashin nasarar dayan 3-0 a cikin Nuwambar 2020.

Aston Villa na fatan cin Arsenal gida da waje a kaka daya karo na ukun, bayan da ta yi hakan a 1992-93 da kuma 2020-21.

Kungiya Arsenal

Arsenal ta yi nasara 10 daga karawa 11 baya a Premier League da cin kwallo biyu a kalla a kowanne wasan, wadda kwallo biyu ya shiga ragarta a fafatawar.

Ta hada maki 31 daga 33 da yake kasa a wasa 11 a lik a 2024, wadda ta yar da maki a Manchester City da suka tashi 0-0 ranar 31 ga watan Maris.

Bukayo Saka yana da hannu a cin kwallo 11 a karawa 11 baya a Premier League, wanda ya ci tara ya bayar da biyu aka zura a raga.

Kungiya Aston Villa

Aston Villa ta yi kan-kan-kan a yawan lashe wasa a Premier League kamar yadda ta yi gabaki dayan kakar bara, saura maki daya ta hada wanda ta samu a 2022/23.

Wasa tara baya ba a doke Villa ba da ta kara da kungiyoyin London a baya, wadda ta yi nasara shida da canjaras uku.

Wasan da Villa ta buga a baya a waje a gidan Manchester City an doke ta 4-1, amma ba ta taba rashin nasara biyu a wasan waje ba a jere tun bayan Mayun 2023.

1 Comment

  • Posted April 14, 2024 7:57 am 0Likes
    by Sadeeq Dan Ustaz

    Da yuwuwar arsenal ta koma mataki na daya, musamman ganin yadda take kokari a wannan shekarar, sannan za’a take wasanne a gidan ta.

Leave a comment