Ko Arsenal za ta koma ta daya a Premier League?

Arsenal da Brighton za su kece raini a Emirates ranar Lahadi a wasan mako na 17 a gasar Premier League.

Gunners tana ta biyu a kan teburi da maki 36 da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool ta daya mai 37.

Ranar ta Lahadi, Liverpool za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan hamayya a Anfield.

Tuni dan kwallon Arsenal, Gabriel Martinelli ya warke wanda rashin lafiya ya hana shi buga wasa da PSV Eindhoven a Champions League ranar Talata.

Emile Smith Rowe ya murmure daga jinya an kuma sa shi a wasan tsakiyar mako a Netherlands.

Sai dai Mohamed Elneny na jinya, wanda ya ji rauni a karawar ta zakarun Turai da Eindhoven.

Ita kuwa Brighton na cike da murna bayan da Evan Ferguson, Bart Verbruggen da kuma Carlos Baleba suka murmure.

To sai dai Ansu Fati, Pervis Estupinan, Tariq Lamptey, Julio Enciso da kuma Solly March na jinya.

Brighton ta ci Arsenal wasa biyar da rashin nasara hudu a fafatawa 12 a Premier League.

Haka kuma Brighton ta yi nasara a wasa uku baya da ta jiyarci Arsenal a Emirtaes har da 3-1 a League Cup a bara.

Wasa ukun da suka kara a bara tsakanin Arsenal da Brighton

Legue Cup Laraba 9 ga watan Nuwamba 2022        

  • Arsenal    1 – 3 Brighton

Premier League Asabar 31 ga watan Disambar 2022

  • Brighton  2 – 4 Arsenal   

Premier League Lahadi 14 ga watan Mayun 2023        

  • Arsenal    0 – 3 Brighton 

Leave a comment