Ko Arsenal za ta doke Bayern a Emirates a Champions League?

Bayern Munich ta ziyarci Arsenal domin buga kwata fainals a Champions League da za su kara ranar Talata a Emirates.

Wannan shi ne wasa na 13 da za su kece raini a tsakaninsu, inda Bayern mai Champions League ta yi nasara shida da canajaras biyu, yayin da Gunners wadda ba ta taba daukar kofin zakarun Turai ba ta ci wasa uku.

Bayanai kan lafiyar ‘yan wasa

Arsenal ba ta da wani sabon dan wasa da ke jinya, har yanzu Jurrien Timber ne bai warware ba.

Ita kuwa Bayern Munich ana tantamar ko mai tsaron ragarta, Manuel Neuer zai iya wasan tare da Leroy Sane da Kingsley Coman da Aleksandar Pavlovic da kuma Noussair Mazraoui.

Wadanda ke jinya kawo yanzu a kungiyar sun hada da Sacha Boey da Bouna Sarr da Tarek Buchmann da kuma Noel Aseko-Nkili.

Bayanai kan haduwar kungiyoyin biyu

Arsenal ta yi rashin nasara a wasa uku baya da Bayern Munich, wadda aka ci 5-1 kowanne, har da 5-1 gida da waje da Bayern ta yi nasarar a 2016/17, shi ne haduwar karshe da suka yi.

Wannan shi ne karo na biyar da kungiyoyin biyu za ta kara a zagayen ziri daya kwale a Champions League, inda kungiyar Germany ta kai zagayen gaba daga hudu daga ciki (2004-05, 2012-13, 2013-14 da 2016-17 – kuma a zagayen ‘yan 16).

Kungiyar Arsenal

Wannan shi ne karon farko da Arsenal za ta buga zagayen quarter-finals a Champions League tun bayan 2009-10, lokacin da tasha kashi da ci 6-3 gida da waje a hannun Pep Guardiola lokacin yana Barcelona.

Wasa biyu daga bakwai baya da Gunners ta buga a Champions League zagayen quarter-final ta kai fafatawar gaba a ko dai European Cup ko kuma Champions League.

Bukayo Saka yana da hannu a cin kwallo bakwai a wasa bakwai a Champions League, wanda ya ci uku ya bayar da hudu aka zura a raga a kakar nan.

Dan wasan da yake da hannu a cin kwallaye da yawa a kaka daya a Aarsenal a gasar zakarun Turai shi ne Alexis Sanchez a 2015-16 (wanda ya ci uku ya kuma bayar da biyar aka zura a raga).

Kungiyar Bayern Munich

Bayern ta yi rashin nasara biyu a irin wannan matakin a Champions League (3-0 a wasa da Manchester City da 1-0 a karawa da Lazio).

Ta taba yin rashin nasara uku a waje a jere shi ne tsakanin Afirilun 2009 zuwa Aafirilun 2010, wadda ta yi rashin nasara a hannun Barcelona da Fiorentina da kuma Manchester United.

Harry Kane ya ci Arsenal kwallo 14 daga karawa 19 da ya fuskanci kungiyar, cikin kungiyoyin da dan kwallon Bayern ya zurawa kwallo da yawa a raga sun hada da Leicester (20) da kuma Everton (16).

Leave a comment