Kane ya haura Muller a tarihin cin kwallaye a Bundesliga

Harry Kane ya zama na farko a Bundesliga da ya ci kwallo 18 a wasa 12 da fara kakar bana a Bayern Munich.

Hakan na nufin kyaftin din tawagar Ingila, ya haura tarihin da Gerd Muller ya kafa na Bayern Munich mai 17 a raga a karawa 12 a 1968/69.

Kane, wanda ya ci Cologne 1-0 ranar Juma’a ya zama na farko daga Ingila da ya zura kwallo 18 a Bundesliga.

Tsohon dan wasan Borussia Dortmund, Jadon Sancho, shi ne ke rike da tarihin a baya mai 17 a raga 2019-20.

Bayern Munich, wadda take jan ragamar teburin rukunin farko a Champions League za ta karbi bakuncin Copenhagen ranar Laraba 29 ga watan Nuwamba.

Daga nan kuma za ta karbi bakuncin Union Berling a gasar Bundesliga karawar mako na 13 ranar Asabar 02 ga watan Disamba.

Leave a comment