kane ya fara atisaye a bayern munich

Harry Kane ya fara atisaye a Bayern Munich bayan raunin da ya ji, wanda ke fatan buga wa kungiyar Bundesliga ranar Asabar da Borussia Dortmund.

Bayern ta sanar cewar dan kwallon tawagar Ingila ya yi atisaye cikin ‘yan wasan kungiyar, wanda ya ji rauni a wasan da suka doke Darmstadt 5-2 ranar 16 ga watan Maris.

Hakan ne ya sa bai buga wa England wasan sada zumunta da Brazil ranar Asabar da na Belgium ranar Talata ba.

Kane ya ce Dortmund kwallo uku rigis a wasan farko da Bayern Munich ta ci Dortmund 4-0, wanda si ne kan gaba a cin kwallaye a Bundesliga a bana mai 31 a raga.

Bayern tana ta biyu a teburin Bundesliga da tazarar maki 10 tsakaninta da Bayern Leverkusen, saura wasa takwas a kammala kakar bana.

Dortmund tana ta hudu gurbi na karshe na zuwa gasar Champions League, amma tana fuskantar kalubale daga RB Leipzig.

Leave a comment