Kane ya ci kwallo na 36 a Bundesliga ranar Asabar

Harry Kane ya ci kwallo na 36 a Bundesliga a bana, amma Bayern Munich ta yi rashin nasara 3-1 a gidan Stuttgart.

Kyaftin din tawagar Ingila ya farke kwallon da aka fara zura musu a raga a bugun fenariti a minti na 37, bayan da aka yi wa Serge Gnabry keta.

Stuttgart ce ta fara cin kwallo ta hannun Leonidas Stergiou ta farko da ya ci a Bundesliga kenan, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Jeong Woo-yeong ya kara na biyu, sannan Katompa ya zura na uku a raga.

Wannan shi ne karon farko da Stuttgard ta doke Bayern Munich a gida tun 2007, wadda ke fatan samun gurbin shiga Champions League a badi.

Da wannan sakamakon Bayern Leverkusen, wadda ta lashe Bundesliga na bana tana da maki 81, sai Bayern Munich ta biyu mai maki 69 da kuma Stuttgard ta uku da 67.

Kwallon da Kane ya ci saura biyar ya yi kan-kan-kan da Robert Lewandowski, wanda yake da tarihin cin 41 a kaka daya a Bundesliga, kuma saura wasa bibiyu a kammala kakar nan.

Kane ya koma buga Bundesliga a bana daga Tottenham.

Leave a comment