Kane ya ci kwallo na 33 a Bundesliga a wasa da Berlin

Harry Kane ya ci kwallo na 33 a Bundesliga, yayin da Thomas Mueller ya zura biyu a raga a wasan da Bayern Munich ta je ta dura 5-1 a ragar Union Berlin ranar Asabar.

Mako daya kenan da Bayern Leverkusen ta lashe Bundesliga na bana a karon farko a tarihi, sannan ta takawa Bayern Munich burki, wadda ta lashe kofin 11 a jere.

Kane ne ya ci kwallo na biyu, sannan ya bai wa Mathys Tel ya zura na hudu a raga, kenan dan wasan tawagar England yana da hannu a cin kwallo 51 a kakar nan a dukkan fafatawa.

A gasar ta Bundesliga, saura kwallo takwas Kane ya yi kan-kan-kan da Robert Lewandowski a tarihin yawan cin kwallaye a babbar gasar gasar tamaula ta Germany a kaka daya.

Leon Goretzka ne ya fara ci wa Bayern kwallo a minti na 29 da fara wasan, yayin da Muller, wanda ya buga wasa na 470 a Bundesliga ya zura biyu a raga, Berlin ta zare daya daf da za a tashi ta hannun Yorbe Vertessen.

Union, wadda ta fafata da Real Madrid da Napoli a Champions League a kakar nan ta ci wasa daya daga takwas baya, sannan tana da tazarar maki uku tsakanintda da gurbin masu bari Bundesliga a bana.

Leave a comment