Kane ya ci Arsenal kwallo na 15 daga wasa 20

An tashi 2-2 tsakanin Arsenal da Bayern Munich a wasan farko zagayen quarter finals a Champions League ranar Talata a Emirates.

A minti na 12 da take leda Arsenal ta ci kwallo ta hannun Bukayo Saka daga baya Bayern ta farke ta hanun Serge Gnabry, kafin hutu Harry Kane ya kara na biyu a bugun fenariti.

Kyaftin din tawagar England ya ci Arsenal kwallo na 15 daga wasa 2o da ya fuskanci Gunners har da haduwa a Premier League kafin ya koma Bayern Munich kan fara kakar bana daga Tottenham.

Leandro Trossard ne ya farkewa Gunners kwallon, kenan sai a gidan Bayern Munich a Germany za a tantance wadda za ta kai daf da karshe a Champions League a bana.

Bayern Munich mai Champions League shida jimilla za ta karbi bakuncin Arsenal mai fatan daukar na farko a tarihi ranar Laraba 17 ga watan Afirilu.

Leave a comment