Kane ba zai buga wasan karshe a Bundesliga ba

Harry Kane ba zai yi wa Bayern Munich wasan karshe a gida a Bundesliga da za ta kara da Wolfsburg ba, wanda ke fama da ciwo baya.

Wannan raunin ne ya sa ya fita a Champions League a karawa da Bayern Munich ta yi rashin nasara a Real Madrid a wasan daf da karshe ranar Laraba a Spain.

Bayern za ta koma mataki na biyun teburi da zarar ta ci Wolfsburg ranar Lahadi, bayan da zai rage saura wasa biyu kenan.

A minti na 85 aka shire Kane a Champions League karawar daf da karshe, inda Real ta ci wasan ta dakile mafarkin Bayern na buga wasan karshe a kofin zakarun Turai na bana.

Bayan tashi daga wasan Real Madrid Thomas Tuchel ya sanar cewar Kane ya dade yana buga wasan da ciwon baya, wanda lokaci ya yi da ya kamata ya yi jinya.

Kane ya ci wa Bayern kwallo 44 a kakar nan, karon farko da ya sharara kwallaye da yawa a kaka daya, wanda bai taba lashe babban kofi ba a tarihin sana’arsa ta tamaula.

Kyaftin din England shi ne kan gaba a yawan zura kwallaye a raga a Bundesliga mai 36 da tazarar 10 tsakaninsa da Serhou Guirassy na Stuttgart.

Tuchel ya ce Leroy Sane da Jamal Musiala da kuma Serge Gnabry na jinya, ya kara da cewar da kyar idan za su buga wa kungiyar wasan karshe ranar Asabar 18 ga watan Mayu da Hoffenheim.

Leave a comment