Tawagar Italy national football team ta doke Northern Ireland national football team da ci 2-0 a wasan neman gurbin shiga gasar FIFA World Cup 2026 da suka buga ranar Alhamis.
Italy ta fara cin ƙwallo ne ta hannun Sandro Tonali, ɗan wasan Newcastle United, a minti na 56, kafin Moise Kean ya ƙara ta biyu saura mintuna 10 a tashi daga wasan.
Da wannan sakamakon, Italy ƙarƙashin jagorancin koci Gennaro Gattuso za ta fuskanci Bosnia and Herzegovina national football team ranar Talata, inda duk wadda ta yi nasara za ta samu tikitin zuwa gasar kofin duniya da za a yi a Amurka, Canada da Mexico.
Rabonda Italy ta halarci gasar kofin duniya tun a shekarar 2014, bayan da ta kasa samun tikitin shiga gasar FIFA World Cup 2018 da kuma FIFA World Cup 2022.
A gefe guda, Northern Ireland national football team ta yi fatan komawa gasar kofin duniya a karon farko cikin shekaru 40, wanda zai kasance karo na huɗu a tarihinta.
Haka kuma, Northern Ireland za ta buga wasan sada zumunta da Wales national football team a Cardiff, duk da cewa ba su samu tikitin shiga gasar ba.
Duk wadda ta yi nasara tsakanin Italy da Bosnia-Herzegovina za ta shiga rukuni na B a gasar FIFA World Cup 2026 tare da Canada da Switzerland da kuma Qatar.
