Juventus za ta dauki Greenwood

Watakila Juventus ta dauki dan kwallon Manchester United, Mason Greenwood da zarar an kammala kakar bana.

Mai shekara 22 wanda ke buga wasannin aro a Getafe a Spain, na taka rawar gani a La Liga a kakar nan, wanda ya ci kwallo takwas ya kuma bayar da biyar aka zura a raga.

Ana ta rade-radin kungiyoyi da dama na son daukar matashin dan kasar Ingila, bayan da sabon wanda ya sayi wani kaso a hannun jarin United, Sir Jim Ratcliffe ya ce kofa a bude take ga Greenwood.

Shekara biyu da ta wuce an tsare Greenwood, bayan da wata mata ta shigar da korafin an yi mata fyade da cin zaarafinta, wanda aka tuhuma har da barazar yin kisa.

To sai dai a watan Fabrairun bara aka soke dukkan tuhume-tuhumen da ake masa, har ya yi niyar komawa taka leda a kungiyar Old-Trafford, amma magoya baya ba su amince ba.

Hakan ne ya sa United ta bayar da aronsa ga Getafe, wanda kawo yanzu ke taka rawar gani a fafatawa 24 da ya yiwa kungiyar da ke buga La Liga a Spain.

Kawo yanzu United ba za ta sake bayar da aron da kwallon ba, wanda yake da sauran yarjejeniyar da za ta kare zuwa Yunin 2025, kenan sai dai ta sayar da shi kai tsaye.

Bayan da ake cewa Juventus na son sayen dan kwallo, itaka Atletico Madrid da Barcelona, duk suna fatan sayen dan wasan.

Leave a comment