Ƙungiyar Juventus mai buga Serie A na fatan ɗaukar Antonio Rudiger daga Real Madrid.
Yarjejeniyar Rudiger za ta kare a karshen kakar bana, wasu na cewa watakila a tsawaita masa kaka ɗaya nan gaba.
Juventus na jiran ɗaukar ɗan ƙwallon tawagar Jamus, domin ya sake buga Serie A a karo na biyu.
Ƙungiyar Italy na sa ran bai wa Rudiger ƙunshin kwantiragin kaka biyu, domin ya koma Italy da taka leda.
idan hakan ta tabbata zai sake aiki karkashin koci, Luciano Spaletti bayan da ya horar da shi a Roma.
Wasu rahotannin na cewar tuni Juventus ta zauna da wakilin Rudiger, domin cimma matsaya.
Haka shima David Alaba yarjejeniyarsa za ta kare a Real Madrid a karshen kakar nan.
Daman ya yi fama da jinya a ƙungiyar, tun bayan da ya koma can daga Bayern Munich.
Real Madrid za ta karɓi bakuncin Atletico Madrid a wasa na biyu a La Liga da za su kara a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.
Karo na uku da za su kece raini, bayan da Atletico ta ci 5-2 a La Liga, Real Madrid ta yi nasara 2-1 a Spanish Super Cup a Saudiyya.