Juventus ta dauki Coppa Italiya na bana na 15 jimilla, bayan doke Atalanta 1-0 ranar Laraba a Stadio Olimpico.
Dan wasa Dusan Vlahovic ne ya ci wa Juentus kwallon da ta samu damar lashe kofin, wadda ita ce kan gaba a ywan daukar Coppa Italia a tarihi.
Juventus ended a three-year wait for a trophy as Dusan Vlahovic’s early goal secured a 1-0 win over Atalanta in the Coppa Italia final at the Stadio Olimpico.
Wannan karawar maimaicin wadda suka yi ce a gasar a 2021, wadda Juventus nan ma ita ce ta cinye wasan.
To sai dai kociyan Juventus, Massimiliano Allegri ya karbi jan kati a fafatawar.
Atalanta za ta buga wasan karshe da Bayern Leverkusen a Europa League a cikin watan nan, bayan da kungiyar Germany ta yi wasa 50 a jere ba tare da an doke ta ba a dukkan karawa a bana.
Wannan shi ne karo na uku da kungiyoyin suka kara a kakar nan, inda a Serie A aka tashi 0-0 a gidan Atalanta, sannan suka yi 2-2 a Juventus.
Juventus tana mataki na hudu da maki 67 a teburin Serie A da tazarar maki hudu tsakani da Atalanta ta biyar din teburi.
Jerin wadanda suka dauki Coppa Italiya a tarihi:
- Juventus FC – 15
- Inter Milan – 9
- AS Roma – 9
- SS Lazio – 7
- SSC Napoli – 6
- ACF Fiorentina – 6
- AC Milan – 5
- Torino FC – 5
- UC Sampdoria – 4
- Parma Calcio 1913 – 3
- Bologna FC – 2
- Vicenza – 1
- Atalanta BC – 1
- Venezia – 1
- Genoa CFC – 1
- Vado Football Club 1913 – 1