Juventus na son sayen Jadon Sancho

Wasu jaridu na cewa Juventus tana sawun gaba daga cikin masu son sayen dan wasan Manchester United, Jadon Sancho.

Ana cewa dan kwallon tawagar Ingila zai bar Old Trafford a Janairu, bayan rashin jituwa tsakaninsa da Erik ten Hag.

Rabon da a saka dan kwallon a wasa tun kan wasan Arsenal da United a cikin watan Satumba.

Ten Hag ya ce dalilin da bai saka Sancho a karawar Arsenal ba, saboda baya sa kwazo a wajen atisaye.

Dan wasan ya mayar da martani a kafarsa ta sada zumunta da cewar ana so a dora laifi a kansa, saboda rashin kokarin da kungiyar ke yi.

Ten Hag ya bukaci Sancho ya bayar da hakuri, wanda ya ce ba zai bayar ba, tun daga nan aka cire shi daga ‘yan wasan da ke takawa United leda a bana.

Sancho mai shekara 23 ya koma Man United a 2021 daga Borussia Dortmund, wadda ya ciwa kwallo 50 ya bayar da 64 aka zura a raga a fafatawa 137.

Dan wasan ya ci kwallo 12 ya bayar da shida aka zura a raga a wasa 82 a Man United.

Leave a comment