Juventus na fatan gurbin ‘yan hutun FARKO ba lashe Serie A ba

Koci, Massimiliano Allegri ya bukaci ‘yan wasan Juventus da su cire hankalinsu ga fatan lashe Serie A na bana, bayan da suke shirin ziyartat Salernitana ranar Lahadi.

Nasarar da Inter ta yi na doke Verona ranar Asabar, ya sa an ba ta tazarar maki biyar – amma Allegri na tantamar inda ya kamata ya mayar da hankalin kungiyar a kakar nan kan matakin da ya dace.

A hirar da ya yi da manema labarai, Allegri ya ce abu mafi mahimmaci su kare a gurbin da za su iya buga Champions League a badi.

Juventus za ta buga karawar bayan wasa 13 a Serie A ba tare da an doke ta ba, wadda ta cascara ‘yar karshen teburin 6-1 ranar Alhamis a Coppa Italia.

Allegri ya tabbatar cewar Hans Nicolussi Caviglia zai buga karawar da Salernitana ba, amma Andrea Cambiaso ba lafiya, yayin da Moise Kean ke jinya.

Salernitana za ta buga wasan na ranar Lahadi, bayan da ta yi wasa shida ba tare da nasara ba, amma ta je ta ci Verona 1-0 a makon jiya.

Leave a comment