Dan kasar Brazil, Joelinton ya saka hannu kan yarjejeniya mai tsawo domin ci gaba da taka leda a Newcastle United
Tun farko kwantiraginsa zai kare a kungiyar St James Park a karshen kakar 2025, wanda kadan ya rage a sayar da shi a Janairu in ji koci, Eddie Howe.
Sai dai Joelinton, wanda Newcastle United ta saya a matakin mafi tsaga a 2019 daga Hoffenheim ya ce komwa da ya yi buga Premier League shi ne hukunci mafi amfana da ya ci karo da shi a rayuwa.
Kawo yanzu yana jinya, wanda sai a farkon kaka badi ake sa ran zai murmure ya koma fagen daga.
Steve Bruce ne ya sayo Joelington a matakin mai cin kwallo daga baya Howe ya mayar da shi mai buga tsakaiya, wanda kwazonsa ya sa Brazil ta fara gayyactarsa a 2023
Kawo yanzu Newcastle ba ta fayyace tsayon kunshin yarjejeniyar da ta kulla da Joelinton ba.