Jamus za ta fara wasa da Scotland a Euro 2024

Scotland za ta kara da Jamus a wasan bude Euro 2024, bayan da aka raba jadawalin gasar da za a buga a badi.

Sauran da ke rukunin farko sun hada da Hungary da kuma Switzerland.

England tana rukuni na uku da ya kunshi Denmark da Slovenia da kuma Serbia.

Idan Wales za ta yi nasara a karawar cike gurbi za ta kasance a rukuni na hudu da ya hada da France da Netherlands da kuma Austria.

Cikin watan Maris za a yi wasannin cike gurbi, domin zakulo ukun da za su cike gurbin Euro 2024.

Jamus za ta kara da Scotland a wasan bikin bude gasar a Allianz Arena a Munich ranar Juma’a 14 ga watan Yuni.

Ita kuwa England, wadda ta buga wasan karshe a Euro 2020 za ta fara wasa da Serbia ranar 26 ga watan Yuni.

Italy mai rike da kofin tana rukuni na biyu da ya hada da Spain da Croatia da kuma Albania.

Za a buga wasan karshe a Euro 2024 ranar 14 ga watan Yuli a Berlin a Olympia stadion.

Yadda aka raba jadawalin:

Group A: Germany, Scotland, Hungary, Switzerland

Group B: Spain, Croatia, Italy, Albania

Group C: Slovenia, Denmark, Serbia, England

Group D: Play-off winners A, Netherlands, Austria, France

Group E: Belgium, Slovakia, Romania, Play-off winners B

Group F: Turkey, Play-off winners C, Portugal, Czech Republic

Play-off winners A: Poland, Wales, Finland, Estonia

Play-off winners B: Israel, Bosnia-Herzegovina, Ukraine, Iceland

Play-off winners C: Georgia, Greece, Kazakhstan, Luxembourg

Leave a comment