Mai masaukin baki, Ivory Coast ta sanar da wadanda za su buga mata gasar cin kofi Afirka da za a yi a 2024.
Kamar yadda hukumar kwallon kafar kasar ta sanar ranar Alhamis, ta gayyaci ‘yan kwallo 27 a gasar da za ta fara gudanarwa a cikin watan Janairu zuwa Fabrairu.
Koci, Jean-Louis Gasset ya gayyaci dan wasan Borussia Dortmund, Sebastien Haller da na Monaco, Wilfried Singo.
Sauran sun hada da Ibrahim Sangare mai buga Premier League mai wasa a Nottingham Forest da Seko Fofana (Al Nassr) da kuma Franck Kesslie (Al Ahli).
To sai wasu fitattun ‘yan kwallon da bas u sun hada da mai taka leda a Galatasary Wilfried Zaha da kuma na Beskitas, Eric Bailly.
The Ivory Coast tana rukunin farko da ya hada da Guinea-Bissau da Nigeria da kuma Equitorial Guinea.
Tawagar Ivora Coast:
Masu tsaron baya: Yahia Fofana (Angers/FRA), Charles Folly (Asec Mimosas), Badra Ali (Sekhukhune United/RSA)
Masu tsaron baya: Serge Aurier (Nottingham Forest/ENG), Willy Boly (Nottingham Forest/ENG), Ismael Diallo (Hajduk Split,/CRO), Ousmane Diomandé (Sporting Lisbon/POR), Ghislain Konan (Al-Feiha/KSA), Evans N’dicka (Roma/ITA), Odilon Kossonou (Bayer Leverkusen/GER) Wilfried Singo (Monaco/FRA)
Masu buga tsakiya: Jean-Thierry Amani Lazare (Union Saint-Gilloise/BEL), Idrissa Doumbia (Alanyaspor/TUR), Seko Fofana (Al Nassr/KSA), Ibrahim Sangaré (Nottingham Forest/ENG), Franck Kessié (Al-Ahli/KSA), Jean-Michael Seri (Hull/ENG).
Masu cin kwallo: Simon Adingra (Brighton/ENG), Jonathan Bamba (Celta Vigo/ESP), Jérémie Boga (Nice/FRA), Sébastien Haller (Borussia Dortmund/GER), Karim Konaté (RB Salzburg/AUT), Christian Kouamé (Fiorentina/ITA), Jean-Philippe Krasso (Red Star Belgrade/SRB), Max-Alain Gradel (Gaziantep/TUR), Oumar Diakité (Reims/FRA), Nicolas Pépé (Trabzonspor/TUR)