Ivory Coast ta kafa tarihin yawan cin kwallaye

Ivory Coast ta doke Seychelles 9-0 a Abidjan ranar Juma’a ta kafa tarihin cin kwallaye da yawa a Afirka a wasan neman shiga gasar kofin duniya.

Dan wasan Borussia Dortmund, Sebastien Haller ya fara cin kwallo minti na 20 da fara wasa, sai Karim Konate na Salzburg ya kara na biyu.

Konate da Hamed Traore kowanne ya ci bibiyu a wasan na rukuni na shida.

Wadanda suka zura daya kuwa sun hada Haller da Ibrahim Sangare da Simon Adingra da Seko Fofana da kuma Jean-Philippe Krasso.

Ita dai Seychelles tana ta 195 a jerin kasashen da ke kan gaba a kwallon kafa a duniya, mai tazarar gurbi 121 tsakaninta da Ivory Coast.

Za a buga gasar cin kofin duniya a 2026 a Amurka da Mexico da kuma Canada.

Kafin nan Ivory Coast za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka daga Janairu zuwa Fabrairun 2024.

Leave a comment