Italy ta samu gurbin shiga Euro 2024 a Jamus

Mai rike da kofin nahiyar Turai, Italy ta samu tikitin shiga Euro 2024, bayan da ta tashi 0-0 da Ukraine ranar Litinin.

Tun kan wasan da suka buga a Jamus, Italy na neman koda canjaras ne, ita kuwa Ukraine na bukatar cin karawar.

Ukraine ta yi korafin samun fenariti duk da cewar dan wasan Italy, Bryan Cristante ya taba Mykhailo Mudryk daf da za a tashi daga fafatawar.

Wannan karon Italy, mai rike da Euro 2020, wadda ta kasa zuwa kofin duniya a 2018 da 2022 za ta buga Euro 2024 a Jamus.

Ukraine na buga wasanninta a Jamus, sakamakon hare-haren da Rasha ke kai mata.

Italy ta doke Ingila a bugun fenariti ta lashe Euro 2020 a Wembley.

Ingila ce ta ja ragamar rukuni na uku da maki 20, bayan wasa 10, sai Italy ta biyu da maki 14.

Ukraine, wadda za ta buga wasannin cike gurbi itama maki 14 ne da ita da tazarar rarar kwallaye tsakaninta da Italy.

Arewacin Macedonia maki takwas ne da ita da kuma Malta mara maki ta biyar a rukuni na uku.

Leave a comment