Isco ya tsawaita kwantiragi da Real Betis

Real Betis ta sanar cewar Isco ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a kungiyar zuwa karshen kakar 2027.

Dan wasan ya koma Betis daga abokiyar hamayya Sevilla, ya ci kwallo biyu a karawa 17 da ya yi a LaLiga

Tsohon dan wasan Real Madrid, kashin bayan kungiyar da Manuel Pellegrini ke jan ragama ne, bayan da Betis take ta bakwan teburi, wadda za ta ziyarci Celta Vigo a mako mai zuwa.

Isco mai shekara 31, bai sake samun goron gayyatar buga wa Spain wasa ba tun daga 2019, bayan da wasanninsa ya yi kasa sosai a Real Madrid.

Leave a comment