Iraola ya kara tsawaita yarjejeniyarsa a Bournemouth

Kociyan Bournemouth, Andoni Iraola ya saka hannu kna yarjejeniyar wata 12, domin ya ci gaba da horar da kungiyar zuwa karshen kakar 2025/26.

Iraola mai shekara 41 ya koma kungiyar da horar da tamaula kan yarjejeniyar kaka biyu a Yunin 2023, wanda ya fara tafiyar hawainiya, yanzu ya kai ta matakin da ba ta taba takawa ba a gasar Premier League.

Bournemouth tana ta 11 a teburi da maki 48 za kuma ta kara da Chelsea a Stamford Bridge a wasan karshe a Premier League ta bana ranar Lahadi.

Irola ya koma Bournemouth daga Rayo Vallecano ta Spain, bayan da ta kori Gary O’Neil a karshen kakar da ta wuce.

Ya fara kakar bana da fuskantar kalubale daga baya ya samu maki daga karawa tara daga nan suka yi wasa bakwai ba tare da nasara ba, har da doke Manchester United 3-0 a Old Trafford.

Iraola ne ya lashe kyautar gwrazon kociyan Premier na watan Maris, bayan doke Burnley da Luton Town da kuma Everton, yana cikin ‘yan takarar gwarzon mai horar da Premier League na kakar nana.

Leave a comment