Inter ta ce Inzaghi ba zai koma horar da Liverpool ba

Kungiyar Inter Milan ta ce kociyanta, Simone Inzaghi zai ci gaba da jan ragamarta, ba zai koma Bayern Munich ba da horar da tamaula.

Inzghi ya dora Inter a turbar lashe Scudetto na farko a wajensa na 20 a kungiyar tun bayan da ya maye gurbin Antonio Conte a 2021.

Mai shekara 48 ya lashe Coppa Italia da Italian Super Cups biyu a Lazio, daga baya ya koma jan ragamar Inter, wadda ke bukatar cin wasa daya a Serie A, sai a bata kofin kakar nan.

A kaka biyu da ya fara jan ragamar Inter, Inzaghi ya dauki Coppa Italia biyu da Italian Super Cups biyu da kai kungiyar wasan karshe a Champions League a bara.

Inter wadda take ta daya a teburin Serie A da tazarar maki 14 za ta fafata da ta biyu AC Milan a San Siro a wasan hamayya, inda Inzaghi ya ci 5-1 a wasan farko cikin Satumbar 2023.

Kwazon da Inzaghi ke yi a Inter ya sa ake alakanta shi da karbar ragamar Liverpool, domin maye gurbin Jurgen Klopp, wanda zai hakura da aikin a karshen kakar nan.

Inzaghi wanda yake da sauran kunshin kwantiragi da Inter Milan zuwa karshen Yunin 2025, na fatan daga kofin Serie A na farko ranar Litinin idan har ya doke AC Milan.

Tuni Liverpool ta ci gaba da neman kociyan da zai ja ragamarta a badi, inda aka cewa mai horar da Sporting Lisborn, Ruben Amorin ne za a bai wa aikin.

Tun farko Liverpool ta tuntubi, Vabi Alonso, wanda ya sanar da cewar zai ci gaba da jan ragamar Bayern Leverkusen, wanda ya lashe Bundesliga na farko a tarihin kungiyar, sannan ya takawa Bayern Munich burki, bayan cin 11 a jere.

Wasu kociyan da ake alakanta su da karbar aikin kocin Liverpool sun hada da Roberto De Zerbi na Brighton da na Atalanta, Gian Piero Gasperini, har da tsohon kociyan Wolfsburg, Niko Kovac.

Leave a comment