Inter Milan ta lashe Serie A na 20 jimilla

Inter Milan ta lashe Serie A na bana na 20 jimilla, bayan da ta doke abokiyar hamayya AC Milan 2-1 ranar Litinin.

Wasa ne na hamayya da aka yi a San Siro da ake kira Derby della Madonnina tsakanin Milan da Inter.

Inter ce ta fara cin kwallo ta hannun Francesco Acerbi daga baya Marcus Thuram ya kara na biyu a raga.

Dan wasan tawagar Ingila, Fikayo Tomori ne ya zarae daya a karawar ta babbar gasar tamaula ta Italy.

An bayar da jan kati uku a karawar daf da za a tashi daga wasan na hamayya, inda aka kori dan wasan Milan, Theo Hernandez da na Inter, Denzel Dumfries da kuma kyaftin din Milan.

Ana busa tashi ‘yan wasan Inter suka dinga sufa a cikin fili ta murnar lashe Scudetto na 20 jimilla, inda sune bakin Inter a San Siro.

Inter ta lashe kofin saura wasa biyar a kammala Serie A ta kakar nan da tazarar maki 17 tsakaninta da Milan ta biyun teburi,

Wannan shi ne karon farko da aka ci Serie A cikin wasan hamayya a Milan Derby a karawa ta 116 tsakaninsu.

Kenan Inter ta dauki Scudetto na 20, yayin da Milan take da 19, Juventus ce ta daya a yawan lashe kofin mai 22 jimilla.

Wannan shi ne karo na biyu da Inter ta dauki Serie A tun bayan 2010 karkashin Antonio Conte a 2021.

Simone Inzaghi ya dauki Serie A na farko kenan a tarihin horar da tamaula, kuma saura wasa biyar a kammala kakar nan, inda Inter ta yi karawa 27 ba tare da an doke ta ba.

Ta kuma ci kwallo 79 an zura mata 18 a lik a bana.

Inter Milan ta yi nasara shida kenan a wasan hamayya a kan Milan, kamar yadda Milan ta yi a kan Inter tsakanin 1911-1913 zuwa 1946-1948.

Leave a comment