Inter Milan na son daukar Martial da Broja

Inter Milan na duba yiwuwar daukar dan kwallon Manchester United, Anthony Martial da na Chelsea, Armando Broja.

Inter, wadda ta kai wasan karshe a bara a Champions League tana taka krawar gani a bana, wadda ita ce ta daya a kan teburin Serie A.

Kungiyar da Simone Inzaghi ke jan ragama ta bai wa Juventus tazarar maki hudu ta biyun teburin Serie A.

A kwazon da Inter take yi a bana bayan wasa 17 ta ci kwallo 41, kuma bakwai ne suka shiga ragarta.

Cikin tarin kwallayen da ta ci a bana, ‘yan wasa uku ne suka fi ci mata su, da ya hada da Lautaro Martinez da Marcus Thuram da Hakan Calhanoglu da tsakaninsu suka ci 29.

Yayin da tsakanin Marko Arnautovic da kuma Alexis Sanchez da ake sa ran za su ci mata kwallaye da yawa, sun shiga wasa 15 a tsakaninsu a canji dan kwallo.

Arnautovic na fama da jinya a kakar nan – kamar yadda

Gazzetta dello Sport, Inter na duba ‘yan wasan da za ta dauka a Janairu, domin ta kara karfin wasanninta.

Martial na Manchester United da Broja na Chelsea suna cikin wadanda take son dauka a Janairu, saboda halin da suka tsinci kansu a kungiyoyinsu a kakar nan.

Wasa bakwai aka fara da Martial da 12 da ya shiga canji, wanda ya ci kwallo biyu kacal, amma Man United na sa ran tsawaita kwantiraginsa zuwa 2025.

Shi kuwa Broja baya buga wasanni sosai, tun bayan da ya warke daga ciwon gwiwa.

Wasa hudu kacal dan kasar Albania ya yi da shiga canji sau bakwai da cin kwallo daya a cikin watan Oktoba.

Sai dai Chelsea za ta amince ta bayar da aron dan kwallon ne, idan ta samu madadinsa.

Ranar Laraba Chelsea wadda take ta 11 a teburi za ta karbi bakuncin Crystal Palace ta 15 a wasan mako na 19 a Premier League a Stamford Bridge.

Leave a comment