Inter Miami za ta je Tokyo wasan sada zumunta

Kungiyar da Lionel Messi ke buga wa tamaula, Inter Miami ta sanar cewar za ta kara da mai rike da kofin gasar Japan, Vissel Kobe.

Kyaftin din Argentina zai ja ragamar kungiyar da ke buga kwallon Amurka, MLS a katafaren filin kasar mai cin ‘yan kallo 60,000 da za su kara ranar 7 ga watan Fabrairu.

Wannan wasan yana daga cikin shirin da kungiyar ke yi na tunkarar gasar Amurka a kaka ta gaba.

Tun kan Inter Miami ta ziyarci Japan, za ta fara wasa biyu a Saudia Arabia da kuma Hong Kong.

Vissel Kobe tsohuwar kungiyar Andres Iniesta ce, wanda zai je kallonon wasan, domin ya gana da Messi da Sergio Busquets da kuma Jordi Alba da ke Inter Miami, tsoffin ‘yan wasan Barcelona.

‘Yan wasan sun lashe Champions League da La Liga hudu a kungiyar Spain, yayin da Iniesta da Busquets suka dauki kofin duniya a Spain.

Inter Miami za ta fara a wasa a 2024 da sada zumunta da El Salvador ranar 19 ga watan Janairu.

Daga nan ta je Saudi Arabia ranar 29 ga watan Janairu domin fuskantar Al-Hilal.

Ranar 1 ga watan Fabrairu za ta kece rainin da Al-Nassr, kungiyar Cristiano Ronaldo kenan.

Daga nan ne sai ta je Hong Kong ranar 4 ga watan Fabrairu, sai kuma ta je Japan.

Leave a comment