Ilele ya ragargaji Bahagon Ali Kawoji a Maraba

Ilele Garkuwan mai caji da Bahagon Ali Kawoji sun fafata a damben safe a Marabar ‘Nyanya ranar Lahadi.

Wato a gidan wasa na Idris Bambarewa da ke ‘yan tifa a Marabar ‘Nyanya.

A wasannin da aka yi don ajon Autan na Aisha, Ilele dan damben Kudu yafi nuna kwazo fiye da dan wasan Guramada Bahagon Ali Kawoji.

Turmi biyu suka yi ba kisa, alkalin wasa Anas dan Dume ya raba su.

Dambe daya ne ya yi kisa, shi ne wanda Shagon Bisi ya buge Shagon Yalo, sauran canjaras aka yi.

Wasannin da aka yi canjaras:

  • Manun Garkuwa da Dan Aliyu
  • Dogon Mamman da Garkuwan Yahayan Tarasa
  • Garkuwan Duna da Dogon Awilo
  • Shagon Nokiya da Shagon na Jimama
  • Shagon Autan dan Bunza da Shagon Bahagon Buma
  • Shagon Fatalwa da Bahagon Yahayan Tarasa
  • Ushu da Manun Garkuwa
  • Dogon Awilo da Shagon Autan dan Bunza

Leave a comment