Hull City ta raba gari da kociyanta Rosenior

Hull City ta kori Liam Rosenior bayan da kungiyar ta kasa samun gurbin shiga wasannin da zai ba ta damar zuwa Premier League daga Championship.

Rosenior, wanda ya saka hannun kaka uku a Disambar 2023, ya ja ragamar kungiyar zuwa mataki na bakwai a Champions League, kwazo mafi girma tun bayan 2016.

Ranar Asabar Plymouth ta ci Hull City 1-0, hakan ya sa ta kasa samun matakin cike gurbi da tazarar maki uku tsakani.

Sai dai kwazon da Rosenior ya yi a bana, yana cikin wadanda ke takarar gwarzon kociya a Championship, inda mai horar da Ipswich, Kieran McKenna ya lashe kyautar.

Rosenior, mai shekara 39, wanda ya ja ragamar kungiyar wata 18, ya yi kaka biyar a Hull a matakin dan wasa, wanda ya bayar da gudunmuwar da ta samu gurbin shiga Premier League a 2013.

Ya koma aikin koci a kungiyar da ke MKM Stadium, wanda ya maye gurbin Shota Arveladze cikin Disambar 2022, wanda ya yi mataimaki a karkashin Phillip Cocu da Wayne Rooney a Derby County.

Leave a comment