Hukumar kwallon Nigeria ta bai wa Manu Garba Golden Eaglets

Hukumar kwallon kafa ta Nigeria, NFF ta bai wa Manu Garba aikin kociyan matasa ‘yan kasa da shekara 17 da ake kira Golgen Eaglets.

Wannan shi ne karo na biyu da zai ja ragamar matasan Nigeria, bayan da ya lashe kofin duniya na FiFA U17 a United Arab Emirates a 2013 – kofi na hudu da Nigeria ta dauka a tarihi.

Cikin ‘yan wasan da Garba ya ja ragama suka lashe kofin duniya a 2013 sun hada da Kelechi Iheanacho da Taiwo Awoniyi da Isaac Success da Musa Mohammed da Chidiebere Nwakali da mai tsaron raga, Dele Alampasu.

Matasan ‘yan kasa da shekara 17 da ta yi ta biyu a Africa a Morocco, bayan rashin nasara a bugun fenariti a hannun Ivoty Coast ta fara da doke Mexico 6-1 a gasar kofin duniya.

Sannan ta yi 3-3 da Sweden, sai ta caskara Iraq 5-0 – a zagaye na biyu ta doke Iran 4-1 ta samu nasara a kan Uruguay a quarter finals da ci Sweden 3-1 a daf da karshe da doke Mexico 3-0 a wasan karshe.

Manu Garba tsohon dan wasan tawagar Nigeria ya fara aiki nan take, zai kuma kai matasan Ghana a gasar WAFU U17 da za a yi a watan gobe.

Leave a comment