Holstein Kiel ta hau kan gasar Bundesliga a karon farko

Holstein Kiel ya hau gasar Bundesliga a karon farko a tarinta, bayan tashi 1-1 da Fortuna Duesseldorf ranar Asabar.

Kungiyar ta yi wannan fafutukar tun daga gasar Germany ta rukuni na hudu zuwa Bundesliga cikin kaka 10.

Kiel ta yi wannan namijin kokrin daga Arewacin kasar kuma ta hudu da ta kai Bundesliga cikin kaka 11 tun daga karamar gasar.

Tun a baya kungiyar ta kusan samun gurbin shiga Bundesliga sau biyu a baya, wadda ta kare a mataki na 2017 da kuma 2020/21, wadda ta yi rashin nasara a wasannin cike gurbi.

Haka kuma St Pauli ta samu damar shiga Bundesliga, bayan kaka 13 tana ta fata, bayan da ta yi nasara a VfL Osnabrueck ranar Lahadi da yammci.

Haka kuma nasarar da St Pauli ta samu ya sa ta hau kan Kiel da tazarar maki daya, sai dai rashin nasara da Fortuna Duesseldorf’ ta yi a wasa da Kiel ya sa ta rasa gurbin shiga Bundesliga kai tsaye, sai dai ta yi wasannin cike gurbi.

Leave a comment