Har yanzu Real Madrid ba ta hakura da neman Arnold

Har yanzu Real Madrid na son sayen dan kwallon tawagar England, Trent Alexander-Arnold daga Liverpool. (Fabrizio Romano via Football365

Kociyan Bayer Leverkusen, Xabi Alonso na fayan nan gaba zai horar da kungiyoyin da ya taka leda wato Liverpool da Real Madrid da kuma Bayern Munich. (Abendzeitung – in German)

Batun daukar da Bayern Munich ke son yi na kociyan Crystal Palace, Oliver Glasner ya yi sanyi, bayan da aka sanar da kungiyar dake buga Bundesliga cewar kudin daukar mai horarwar zai kai £86m daga Selhurst Park. (Bild – in German – subscription required)

Napoli ta kara bude damar tattaunawa da Antonio Conte a matakin sabon kociyanta, bayan da ya rage yawan albashin da yake buri karba tun farko, kuma AC Milan ma na sha’awar sayen tsohon kociyan Chelsea da Tottenham. (Il Mattino – in Italian – subscription required)

Kungiyoyin dake buga gasar Saudi Pro League na son daukar ‘yan wasan Manchester United biyu da ya hada da Casemiro da kuma Bruno Fernandes. (Telegraph – subscription required)

Arsenal are set to lose promising defender Reuell Walters, 19, after the England U20s international rejected the offer of a fresh contract to pursue opportunities elsewhere. (Athletic – subscription required)

Sevilla da Sergio Ramos na tattaunawa da San Diego, domin tsohon dan kwallon Real Madrid ya koma Major League Soccer (MLS). (Athletic – subscription required)

Chelsea na duba ‘yan wasan da za at dauka a badi domin cike gurbin mai tsaron baya daga hagu da mai cin kwallaye da mai tsare baya daga tsakiya. (Telegraph – subscription required)

Leave a comment