Har yanzu Liverpool na fatan lashe Premier League

Liverpool ta doke Fulham 3-1 a wasan mako na 34 a Premier League da suka kara a Craven Cottage ranar Lahadi.

Liverpool ce ta fara cin kwallo ta hannun Trent Alexander-Arnold a bugun tazara, kuma karo na shida a wannan bajintar a Premier League a bana, wanda ke gaban shi a irin wannan kwazon a kaka daya a Liverpool shi ne Jamie Redknapp (8) da kuma Steven Gerrard (7).

Daga baya Fulham ta zare daya ta hannun Timothy Castagne, bayan da wasa ya nutsa kungiyar Anfield ta kara na biyu ta hannun Ryan Gravenberch da kuma Diogo Jota da ya zura na uku a raga.

Kwallo na 100 kenan da Jota ya ci a dukkan fafatawa, wanda ya ci 44 a Wolverhampton da zura 56 a Liverpool.

Da wannan sakamakon Liverpool ta farfado da damar kara daukar wani kofin a kan Carabao, bayan da Jurgen Klopp zai bar horr da kungiyar a karshen mako.

    Liverpool ta ci karo da koma bayan, sakamakon da Manchester United ta fitar da ita a FA Cup, sannan ta yi duro da United a Old Trafford a Premier League, sai kuma Crystal Palace ta doke ta 1-0 a Anfield a babbar gasar tamaula ta England.

    Daga nan kuma Liverpool ta yi rashin nasara 3-0 a gida a hannun Atalanta a Eurropa League, wadda ta fitar da ita a zagayen quarter finals, duk da cin 1-0 a Italy ranar Alhamis.

    Nasarar da Liverpool ta samu a Craven Cottage ya sa ta koma ta biyun teburi da maki 74 iri daya da na Arsenal ta daya da tazarar rarar kwallaye, yayin da Manchester City mai maki 73 take ta ukun teburi.

    Leave a comment