Hansi Flick ya zama gwarzon kociyan watan Maris a La Liga

Kocin Barcelona, Hansi Flick, shi ne gwarzon kociyan watan Maris a gasar La Liga.

Mai horarwar ɗan ƙasar Jamus ya jagoranci Barcelona zuwa nasarori uku a watan, ciki har da doke Athletic Club da ci 1-0, sannan ta lallasa Sevilla da ci 5-2, tare da samun nasara 1-0 a kan Rayo Vallecano.

Flick ya lashe kyautar ne bayan ya doke sauran masu takara da suka haÉ—a da kocin Atletico Madrid, Diego Simeone, da kuma Luis Castro.

A halin yanzu, Barcelona na kan gaba a teburin La Liga, inda take da tazarar maki huÉ—u a kan Real Madrid da ke matsayi na biyu.

Barcelona za ta fafata da Atletico Madrid a wasan La Liga ranar Asabar 4 ga watan Afirilu, kafin su sake haduwa kwanaki huÉ—u bayan haka a gasar UEFA Champions League.

Daga nan, Barcelona za ta karɓi bakuncin Espanyol a La Liga ranar Asabar 11 ga watan Afirilu, kafin ta je gidan Atletico Madrid domin buga wasa na biyu a zagayen kwata fainal na Champions League.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top