Haaland zai fara atisaye ranar Alhamis – Guardiola

Erling Haaland ba zai buga wa Manchester City wasan karshe a cikin rukuni a Champions League ba da ta je Red Stars Belgrade.

A hira da Guardiola ya yi da ‘yan jarida ya sanar cewar ranar Alhamis Haaland zai fara atisaye domin shirin tunkarar Fifa Club World Cup a Saudi Aarabia.

Dan wasan tawagar Norway bai yi wa Man City wasan Premier League da ta doke Luton Town 2-1 ranar Lahadi ba.

Ba a tabbatar da cewar ko dan kwallon zai buga wasan da Man City za ta yi da Crystal Palace ba a Premier League ranar Asabar.

Haka kuma Man City za ta buga wasan na ranar Laraba ba tare da Jeremy Doku da Kevin De Bruyne, wadanda ke jinya.

Rabonda De Bryne ya buga wa Man City tamaula tun cikin watan Agusta, sakamakon jinya da yake yi.

Mai tsaron raga Ederson baya nan, amma za a yi amfani da Stefan Ortega a raga.

Tuni dai Man City ta kai zagaye na biyu a Champions League, Red Star ta yi rashin nasara 3-1 a Etihad cikin Satumba, wadda take ta karshen teburi.

Leave a comment