Haaland ya dora Man City a gurbin lashe Premier na bana

Manchester City ta je ta doke Tottenham 2-0 a kwantan Premier League ranar Talata, inda hakan ya dora kungiyar a kan teburi.

Erling Haaland ne ya ci kwallon biyu kuma na 27 jimilla a bana, yayin da kungiyar Etihad ke fatan lashe na hudu a jere, ba wadda take da wannan bajintar.

Da wannan sakamakon City tana ta daya a kan teburin Premier League da tazarar maki biyu tsakani da Arsenal, kuma ranar Lahadi 19 ga watan Mayu za a buga wasannin karshe

City mai rike da kofin bara na uku jimilla za ta karbi bakuncin West Ham a Etihad, wadda da zarar ta yi nasara, za ta lashe Premier na hudu a jere.

Ita kuwa Arsenal, wadda take ta biyun teburi za ta karbi bakuncin Everton a Emirates, rabon Arsenal da Premier tun 2003/04.

Haka kuma doke Tottenham da aka yi ya sa Aston Villa ta samu gurbin shiga Champions League a badi, bayan da za ta kare a mataki na hudu da za ta wakilci England tare da City da Arsenal da kuma Liverpool.

Ita kuwa Tottenham za ta kara a Europa League tare da ko dai Newcastle ko Chelsea ko kuma Manchester United.

A bara ne City ta lashe kofi uku da ya hada da na Premier da FA Cup da kuma Champions League.

Leave a comment