Haaland ya ci kwallo hudu a karon farko a Premier League

Manchester City ta doke Wolverhampton 5-1 a wasan mako na 36 a Premier League ranar Asabar a Etihad.

Erling Haaland ne ya ci hudu rigis, kuma biyu daga ciki a bugun fenariti, yayin da Julian Alvarez ya kara na biyar a raga, Wolves ta zare daya ta hannun, Hee-Whang Hwang.

Kenan dan kasar Norway ya ci kwallo 25 a Premier League a bana da tazarar biyar tsakani da Alexander Isak na Newcastle da kuma Cole Palmer na Chelsea da kowanne ya ci biyar-biyar.

Haaland ne ya lashe takalmin zinare a bara a matakin wanda ya ci kwallaye da yawa a Premier League, mai 36 a raga.

Wannan shi ne karon farko da Haaland ya ci kwallo hudu rigis a Premier League, tun bayan da ya koma Manchester City daga Borussia Dortmund a bara.

Sai dai ya ci Luton biyar a FA Cup a cikin Fabrairu da kuma RB Leipzig a Champions League cikin Maris a bara.

Haaland shi ne na 87 a jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Premier League, mai kwallo 61 a raga.

Leave a comment