Haaland ya ci kwallo 50 a karacin wasa 48 a Premier

Erling Haaland ya ci kwallo a wasan da Manchester City ta tashi 1-1 da Liverpool ranar Asabar a wasan mako na 13 a Premier League.

Dan wasan tawagar Norway ya ci kwallon a minti na 22 da fara wasan a Etihad.

Daga baya Liverpool ta farke ta hanun Trent Alexander-Arnold, saura minti 10 a tashi wasan.

Kenan karon farko da ya zura kwallo a ragar Liverpool a gasar Premier, tun bayan da ya koma City da taka leda.

Sai dai kafin nan ya ci Liverpool a lokacin da yake taka leda a Red Bull Salzburg a Champions League.

Kawo yanzu Haaland ya ci kwallo a dukkan kungiya 20 da ya fuskanta daga 21, Brentford ce kadai bai ci ba.

Wanda yake na farko a cin kwallo 50 a Premier League a karancin wasanni, shi ne Andrew Cole da ya yi karawa 65.

Alan Shearer ya ci na shi 50 a fafatawa 66, shi kuwa Ruud Van Nistroy a wasa na 68 ya ci kwallo na 50 da Salah da Tottes, wadanda sai da suka yi wasa 72.

Da wannan sakamankon Manchester City ta ci gaba da zama ta daya a teburin Premier League da maki 29.

Ita kuwa Liverpool tana ta biyu da maki 28, kafin sauran kungiyoyi su buga karawar mako na 13.

Leave a comment