Haaland ba zai je Euro 2024 ba

Erling Haaland shi ne ya lashe Premier League da Champions League da FA Cup a bara, amma ba zai je Euro 2024 ba.

Tawagar Norway ta kare a mataki na uku a teburin farko da maki 11, Spain ce ta yi ta daya da maki 21 da Scotland mai 17.

Haaland dan wasan Manchester City ya ci wa Norway kwallo shida daga 14 da ta zura a raga a wasannin neman shiga Euro 2024.

Tawagogin da suka samu shiga Euro 2024 kai tsaye sun hada da Albania da Austria da Belgium da Croatia da Czech da Denmark da England da France da Germany mai karbar baki.

Sauran sun hada da Hungaryda Italy da Netherlands da Portugal da Romania da Scotland da Serbia da Slovakia, Slovenia da Spain da Switzerland da kuma Türkiye

Guda 12 da za su buga karawar cike gurbi sun hada da Bosnia and Herzegovina da Estonia da Finland da Georgia da Greece da Iceland da Israel da Kazakhstan da Luxembourg da Poland da Ukraine da kuma Wales.

Ranar 2 ga watan Disamba za a raba jadawalin wasannin Euro 2024.

Leave a comment