Haaland ba zai buga wa City wasan Brighton ba

Manchester City za ta je gidan Brighton domin buga kwantan Premier League ranar Alhamis.

City mai maki uku da kwantan wasa uku tana ta ukun teburin Premier League da maki 73 da tazarar makidaya tsakani da Liverpool, wadda za ta je Everton ranar Laraba a wasan hamayya.

Arsenal, wadda ta yi wasa hudu ita ce ta daya a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila, wadda ta dura 5-0 a ragar Chelsea ranar Talata a Emirates.

Ita kuwa Brighton mai wasa 32 da kwantai biyu tana ta 10 teburin da maki 44.

To sai dai Erling Haaland ba zai buga karawar ba, wanda zai yi jinya, bayan buga wasa 25 da cin kwallo 20 ya bayar da biyar aka zura a raga.

Haaland bai yi City FA Cup ba karawar daf da karshe da ta ci Chelsea 1-0 ranar Asabar a Wembley, wadda za ta buga wasan karshe da Manchester United cikin watan Mayu.

A bara ne City ta dauki kofin a kan United, bayan da ta ci 2-1, kenan na bakwai jimilla, yayin da kungiyar Old Trafford take da shi 12.

Wasannin da suka rage a gaban Manchester City:

Premier League Lahadi 28 ga watan Afirilu    

  • Nottm Forest   da        Man City        

Premier League Lahadi Asabar 4 ga watan Mayu       

  • Man City         da        Wolves

Premier League Lahadi Asabar 11 ga watan Mayu           

  • Fulham            da          Man City        

Premier League Lahadi Talata 14 ga watan Mayu         

  • Tottenham      da         Man City        

Premier League Lahadi Lahadi 19 ga watan Mayu              

  • Man City         da         West Ham      

English FA Cup  Asbar 25 ga watan Mayu              

  • Man City         da          Man Utd

Leave a comment