Gundogan zai fuskanci Turkiya a karonsa na farko a tarihi

Kyaftin din Jamus, llkay Gundogan zai buga wasan sada zumunta da Turkiya, karon farko da zai fuskanci kasar da aka haifi iyayensa.

Ranar Asabar tawagar Jamus za ta fafata da ta Turkiya a wasan sada zumunta a shirin da take na karbar bakuncin Euro 2024.

Wasan da Jamus ta fuskanci Turkiya a bayan nan shi ne a cikin Oktoban 2020, amma Gundogan bai yi karawar ba.

Dan kwallon zai buga wa Jamus wasa na 72 a fafatawar da za su yi a filin wasa na Olympic a Berlin ranar Asabar.

Gundogan ya fara yi wa tawagar Jamus tamaula a matakin kyaftin din rikon kwarya a Maris din 2019.

Shekara daya baya ya ci karo da cikas, bayan wani hoto da ya dauka da shi da Mesut Ozil da kuma shugaban Turkiya, Racep Tayyip Erdogan.

An caccaki ‘yan wasan biyu da cewar aminan Erdogan ne, kenan bas a saka kwazo a wasannin da suke buga wa Jamus yadda ya kamata.

Shi dai Gundowan ya fayyace dalilinsa, wanda hakan ya say a ci gaba da taka a Jamus, yayin da Ozil ya hakura da yi mata tamaula.

Leave a comment