Guessand na fatan cin karin kwallaye domin Palace ta ɗauke shi

Ɗan wasan da ke buga gaba, Evann Guessand na bukatar bayar da karin ƙwallo biyar a zura a raga, domin Crystal Palace ta kammala sayensa daga Aston Villa.

Guessand ya koma Selhurst Park a watan Janairu a matsayin buga wasannin aro, tare da sharadin cewa za a saye shi kan fam miliyan 28 idan ya cika wasu ka’idoji.

Rahoton Sky Sports ya bayyana cewa ɗan wasan na bukatar ya yi sanadin cin kwallo takwas (ko ya ci da kansa ko ya bayar a zura a raga).

Ya zuwa yanzu, ɗan asalin Ivory Coast mai shekaru 24 yana da uku, bayan da ya ci biyu ya kuma bayar da ɗaya aka zura a raga uku – ciki har da kwallon da ya ci Wolverhampton.

Idan bai kai ga wa’adin da aka gindiya. Palace na da zaɓin sayensa kan fam miliyan 28.5, kuma a yanzu dai ƙungiyar ta nuna niyyar sayensa na dindindin.

Tsohon ɗan wasan Nice ya amince da ƙwantiragin kaka hudu a Palace da zarar an kammala cinikin.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top