Granada ta bar La Liga ta bana ranar Asabar

Granada ta yi ban kwana da gasar La Liga ta bana ranar Asabar, bayan da Real Malorca ta ci Las Palmas 1-0.

Kungiyar da take Andulusia za ta karbi bakuncin Real Madrid ranar Asabar, amma ta yi kasa zuwa gasa mai daraja ta biyu ta Spain, bayan da Giovanni Gonzalez kwallo da Mallorca, wadda ta yi ta biyu a Copa del Rey a kakar nan.

Granada, wadda ta yi wasa 34 tana ta 19 teburi da maki 21, wadda ta ci wasa hudu da canjaras tara aka doke ta 21 da cin kwallo 36 aka zura mata 64 a raga.

Wannan nasara ta sa Mallorca ta yi sama tsakani da ‘yan karshen teburi ta dora matsi a kan Cadiz ta 17, wadda za ta fafata da Getafe ranar Lahadi.

Tun a makon jiya Real Madrida ta lashe La Liga na kakar nan na 36 jimilla, wadda ta kai wasan karshe a Champions League na bana.

Leave a comment