Giroud zai koma Major League daga AC Milan

Dan wasan tawagar France, Olivier Giroud zai bar AC Milan a karshen kakar nan, zai koma buga gasar Major League Soccer.

Mai shekara 37 ya lashe Serie A a 2021/22 da cin kwallo 48 da bayar da 20 aka zura a raga a wasa 130 a kungiyar ta Italy.

Ana sa ran zai koma taka leda a kungiyar Los Angeles, wadda tsohon golan Tottenham, Hugo Lloris ke yi wa wasanni.

It is expected that he will join his international team-mate Hugo Lloris at Los Angeles FC.

Ya koma Milan a 2021 bayan da ya bar Chelsea, wanda ya lashe Champions League da Europa League da kuma FA Cup a kaka hudu a kungiyar London.

A baya ya yi kaka shida a Arsenal da daukar FA Cup da cin kwallo 105 a wasa 253.

Giroud ya zura kwallo 57 a wasa 131 a tawagar France – yana gaban Thierry Henry da yawan cin kwallo shida a tawagar France, shi ne kan gaba a wannan tarihin.

Leave a comment