Giroud zai dau jan ragamar wasa da Dortmund

Ranar Talata AC Milan za ta karbi bakuncin Borussia Dortmund a wasa na biyar-biyar a cikin rukuni a Champions League.

Milan na fatan Oliver Giroud zai dauki alhakin kai kungiyar zagaye na biyu a gasar ta zakarun Turai a San Siro.

Giroud ya daga martabar Milan karo da dama tun bayan da ya koma kungiyar, sama da kaka biyu, musamman lokacin da ake bukatar cin kwallo.

Mai shekara 37 ya ci kwallo takwas a bana, wanda ke fatan kai Milan zagaye na biyu, bayan da suka samu kwarin gwiwar doke Paris St Germain.

Giroud, wanda ke fatan ci gaba da taka leda a Milan ya lashe Serie A a kakar 2022 da kai wa daf da karshe a Champions League a bara.

Borussia Dortmund ce ta daya a rukuni na shida da maki bakwai, sai Paris St Germain mai maki shida ta biyu da AC Milan ta uku da maki biyar da mai maki hudu Newcastle United.

Wasannin da za a buga ranar Talata:

  • Lazio da Celtic
  • Shakhtar Donetsk da Royal Antwerp
  • Feyenoord da Atletico Madrid
  • Young Boys da Crvena Zvezda
  • Manchester City da RB Leipzig
  • Barcelona da Porto
  • AC Milan da Borussia
  • Paris Saint-Germain da Newcastle United

Leave a comment