Germany ta ci wasan sada zumunta biyu a jere

Germany na ci gaba da taka rawar gani a shirin karbar bakuncin Euro 2024 a bana, bayan da ta yi nasara a kan Netherlands a karawar sada zumunta ranar Talata.

Tun kafin nan Germany ta doke France 2-0 ranar Asabar a wasan sada zumunta, sannan ta yi nasarar cin Netherlands 2-1 ranar Talata, inda Niclas Fullkrug ya ci mata na biyun a Jamus.

Tawagar Netherlands ce ta fara zura kwallo ta hannun Joey Veerman daga baya Germany ta farke ta hannun Maximilian Mittelstadt a minti bakwai tsakani.

Wannan shi ne karon farko da koci, Julian Nagelsmann ya yi nasarar cin wasa biyu a jere tun bayan da ya karbi jan ragama.

Za a fara Euro 2024 ranar Juma’a 14 ga watan Yuni a Allianz Arena a birnin Munich inda Germany za ta kara da Scotland.

Sauran da suke rukunin farko da ya hada da mai masaukin baki sun hada da Hungary da kuma Switzerland.

Ita kuwa Netherlands, tana rukuni na hudu da ya kunshi Poland da Austria da kuma France.

Za a karkare Euro 2024 ranar Lahadi 14 ga watan Yuli a filin wasa na Olympiastadion a birnin Berlin.

Leave a comment