Georgia za ta buga Euro 2024 a karon farko a tarihi

Georgia za ta buga gasar cin kofin nahiyar Turai a karon farko a tarihi, bayan da ta samu daya daga gurbi ukun da ya rage na shiga Euro 2024 da za a yi a Jamus.

Itama Ukraine ta samu gurbin da kuma Poland a wasannin da Jamus za ta gudanar daga 14 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Yulin 2024.

Georgia ta yi nasarar cin Iceland 2-1 a ranar Talata a wasan cike gurbi da suka fafata.

Kenan za ta kara a rukuni na shida da ya kunshi Turkey ranar 18 ga watan Yuni daga nan ta fafata da Jamhuriyar Czech ranar 22 da kuma fuskantar Portugal ranar 26 ga watan Yuni.

Ita kuwa Ukraine za ta fafata ne a rukuni na biyar, wadda za ta fara wasa da Romania ranar 17 ga watan Yuni, sai ta fuskanci Slokakia ranar 21 ga watan Yuni da kuma Belgium kwana biyar tsakani.

Za a fara bikin bude Euro 2024 a Munich ranar 14 ga watan Yuni, inda Jamus za ta fafata da Scotland.

Leave a comment