Gasar Saudi Arabia za ta kara zawarcin Mbappe da Salah

Babbar gasar kwallon kafa ta Saudi Arabia za ta ci gaba da zawarcin fitattun ‘yan kwallon kafa a fadin duniya.

Hakan ya fito daga bakin Mike Emenalo, mai kula da dauko ‘yan wasan tamaula zuwa gasar ta Saudi Arabia.

Kamar yadda Fifa ta sanar, kungiyoyin Saudi Arabia sun kashe kudi wajen sayen ‘yan wasa da ya kai fam miliyan 701 kan fara kakar bana.

Kudin da ya haura haka, bayan da dan kwallon Paris St Germain, Kylian Mbappe da Mohamed Salah na Liverpool suka ki komawa gasar.

Tun bayan kammala gasar kofin duniya a Qatar a 2022, Al Nassr ta dauki Cristiano Ronaldo, wanda ya raba gari da Manchester United a watan Disamba.

Wasu fitattun ‘yan kwallon da suka koma buga gasar Saudi Arabia sun hada da Neymar da Karim Benzema da Riyad Mahrez da Ruben Neves da Sadio Mane da sauransu.

Leave a comment