Gasar LaLiga na hutu bayan karawar mako na 18

Gasar LaLiga na yin hutu, domin yin shagulgulan Kirsimeti da na sabuwar shekara, bayan kammala fafatawar mako na 18.

An fara gasar LaLiga ranar 11 ga watan Agustan 2023, wadda kawo yanzu an yi karawa 180 da cin kwallo 180.

Dan wasan Real Madrid Jude Bellingham shi ne kan gaba a cin kwalle mai 13 a raga.

Real Madrid ce ta daya a kan teburi mai maki 45, iri daya da na Girona ta biyu, sai Aatletico Madrid ta uku mai 38.

Barcelona wadda take ta hudun teburi itama maki 38 da ita da kuma Athletic Bilbao mai 35 ta biyar din teburi.

‘Yan ukun karshen teburi kuwa sun hada da Celta Vigo ta 18 da maki 13 da Granda ta 19 da maki 8 da kuma Almeria mai maki biyar ta karshen teburi, wato ta 20.

‘Yan wasan da ke kan gaba a cin kwallaye:

  1. Jude Bellingham Real Madrid 13
  2. Borja Mayoral Getafe 12
  3. Antoine Griezmann Atletico Madrid 11
  4. Artem Dovbyk Girona 11
  5. Alvaro Morata Atletico Madrid 9
  6. Ante Budimir Osasuna 8
  7. Robert Lewandowski Barcelona 8
  8. Inaki Williams Athletic Bilbao 8
  9. Gerard Moreno Villarreal 8

Wasannin mako na 19 a gasar LaLiga

Ranar Talata 2 ga watan Janairu

  • Getafe da Rayo Vallecano       
  • Real Sociedad da Deportivo Alaves
  • Valencia da Villarreal

Ranar Laraba 3 ga watan Janairu

  • Granada da Cadiz   
  • Celta de Vigo da Real Betis     

Ranar Alhamis 4 ga watan Janairu

  • Real Madrid da Real Mallorca
  • Girona da Atletico de Madrid
  • Osasuna da Almeria        
  • Sevilla da Athletic de Bilbao
  • Las Palmas da FC Barcelona

Leave a comment