Garkuwan Cindo na alfahari da kisan da ya yi wa Ali Kanin Bello

An kammala kakar wasa ta damben gargajiya ta bana tun bayan da aka fara azumin watan Ramadan, domin ba a yin dambe idan ba da daddare ba.

Yawanci a irin wannan lokacin ana daina yin wasan har sai lokacin da aka sallata, daga nan ne masu gidajen dambe da ƴan wasa kowa zai koma fagen daga.

To sai dai tun kan nan tsohon Sarkin Dambe Garkuwan Cindo ya ce yana alfahari da kisan da ya yi wa Ali Kanin Bello kan fara azumi.

Ya ce nasara da ya yi kan Ali Kanin Belllo ya samu kuɗi da tarin masoya, musamman bajintar da ya yi a Ogere da kuma a Sokoto da kuma Abuja.

Sai dai Garkuwan ya ce Ali Kanin Bello shima ya buge shi to amma bai yi faɗuwar da sai an tasheshi ba, shi da kansa ke mikewa tsaye.

Ya ce amma duk kisan da ya yi wa ɗan wasan Jamus, sai an yi kanikance an kuma nemo rayuwar Ali Kanin Bello daga baya ya koma cikin hayyacinsa.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top